ABNA24 : Akalla shugabannin kasashen Afrika 10 ne aka tabbatar za su halarci jana’izar marigayin, da kasar za ta gudanar.
Kakakin gwamnatin kasar, Hassan Abbasi ya bayyana, yayin wani taron manema labarai, cewa jana’izar za ta gudana yau Litinin, a filin wasan Jamhuri dake babban birnin Dodoma, wanda kuma zai samu halartar shugabannin kasashen Kenya da Malawi da Sudan ta Kudu.
Ya kara da cewa, sauran shugabannin da za su halarta sun hada da na Comoros da Mozambique da Zimbabwe da Zambia da Namibia da Botswana da kuma Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Hassan Abbasi, ya ce shugabannin kasashen Rwanda da Angola da Burundi kuma, za su samu wakilcin manyan jam’ansu. Ya kara da cewa, wakilai daga hukumomin shiyya ma za su halarci jana’izar.
Za a binne marigayi John Magufuli ne a mahaifarsa ta gundumar Chato dake yankin Geita a ranar 26 ga watan nan na Maris.
John Magufuli mai shekaru 61, ya mutu ne ranar Laraba, sanadiyyar ciwon zuciya, a asibitin Emilio Mzena dake Dar es Salaam, babban birnin hada-hadar tattalin arziki na kasar.
342/